
Watan Agusta yanayin zafi ne a birnin Venshabourg . A wannan lokaci yana da zafi kwarai da gaske . Saboda haka ciyayin dake galibin gonakai sun juya launin kore zuwa launin rawaya . Amma itatuwa da ciyayin dake birnin Venshabourg suna ci gaba da kiyaye launin kore .
A wannan birnin , ko a manya ko a kananan garuruwa na Venshabourg, kusan kowa yana sa riguna daban daban launukan rigunan kuma suna da bambanci . A yanayin sanyi , ko tsofafin mata suna sa manyan rigunan fata masu daraja sosai . Rigunan da matasa suke sanya masu sauki ne , amma mayafin wuya da huluna da takalman da suke sawa iri daban daban ne .
Bugu da kari kuma Yarima Charls da Gimbiya Deanna sun fara yin soyayya ne a birnin Venshabourg.(Ado) 1 2 3
|