
A kan saurari wata magana cewa , Allah ya kiyaye . Da farko dai wakilin Rediyon kasar Sin bai fahinta ba . A farkon shekarar 2006 , shi da takwaransa sun yi yawon shakatawa a kogin Times . Sun taba zuwa birnin London da birnin Yichan da birnin Venshabourg da sauran wurare , sai wakilinmu ya amince wannan magana tana da gaskiya . A lokacin kwanaki 10 da suka yi ziyara a kogin Times , ko a hanyoyin zirga-zirga , ko a kantunan da hotel-hotel da kasuwanni , ko a dakunan cin abinci , ko a filayen jiragen sama da tashoshin motoci , akwai kyakkyawar yarinya mai jawo hankalin mutane tana rawa . Ita siririya ce . Kuma tana da karamin kai da karar hanci da korrayen idanu da farar fata . Ta ci ado amma ba sosai ba . Rigar da take sanye da ita ta zamani ce , Amma duk da haka ta koyi da ilmin gargajiya . Mutane masu yawon shakatawa wadanda suka zo daga wurare daban daban na duniya su kan ce , allah ya ba su kyau .
Wakilin Rediyonmu ya rubuta cewa, a cikin litattafai akwai siffar wannan kyakkyawa . Alal misali , Vinas da Yadinna da Sam Anna da Lida da sauransu duk kyawawa ne.
1 2 3
|