Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-03-10 15:52:22    
Hanyar neman bunkasuwa a ketare da kamfanin kera bus kirar Yutong take bi

cri

"Ba ma kawai kamfanin Yutong yana koyon fasahohin zamani na kera bus da na yadda ake tafiyar da masana'antun kera motoci na kamfanin kera bus na Man Commercial Vehicle da yake daya daga cikin manyan kamfanonin kera bus na sauran kasashen duniya ba, har ma ya ci nasarar kiyaye tamburansa. Wannan abu ne da ya fi kyau."

A shekara ta 2002, kamfanin Yutong da kamfanin Man sun zuba kudaden da suka kai kudin Renminbi yuan miliyan 320 sun kafa wani kamfanin jarin hadin guiwarsu, kuma sun kafa wata cibiyar fasaha a birnin Munich na kasar Jamus. Nauyin da aka dora wa wannan kamfanin hada jari shi ne kera gadaje na manya da matsakaitan bus da kayan gyara kuma da aikin sayar da su. Yanzu yawancin kamfanonin kera manyan bus ba su samu izinin kera gadon manyan bus ba, sabo da haka, kamfanin Yutong ya shiga kasuwar kerawa kuma da sayar da manyan bus da ya kera domin yana da masana'antar jarin hadin guiwa na kera gadajen manyan bus.

Ya zuwa yanzu, yawan manya da matsakaitan bus da kamfanin Yutong yake kerawa ya kai dubu 18 tare da gadajen manyan bus dubu 8 a kowace shekara. Babban burin da kamfanin yake son cimmawa shi ne bayan ya yi kokari cikin shekaru 5 zuwa shekaru 7, yawan kudaden da zai samu zai kai kudin Renminbi yuan biliyan 30 a kowace shekara, kuma zai shiga jerin manyan kamfanonin kera manyan bus 5 a duk fadin duniya. (Sanusi Chen)


1  2  3