Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-03-10 15:52:22    
Hanyar neman bunkasuwa a ketare da kamfanin kera bus kirar Yutong take bi

cri

Bayan da mutanen kamfanin Yutong suka samu kwangila daga Amurka, abu na farko da suka yi shi ne sun fara yin nazari kan ma'aunonin fasahohi da dokokin zirga-zirga da abin ya shafa na kasar Amurka. Mr. Zhang Yaowu wanda ke kula da kasuwar Amurka a kamfanin Yutong, ya ce, "Wannan dokar zirga-zirga ta kasar Amurka tana da shafuffuka wajen 760, na juya ta zuwa harshen Sinanci cikin wajen wata 1. Da farko dai, dole ne mu koyi wasu dokokin Amurka da abin ya shafa. Haka nan kuma, lokacin da muke yin zane-zanen bus nasu, za mu mai da hankali kan wadannan ma'aunonin Amurka."

A hakika dai, ba ma kawai matsalolin doka na kasar Amurka suna matsa wa kamfanin Yutong lamba ba, har ma bambancin al'adu da al'adar yin amfani da bus da abubuwa da yawa sun zama kalubalen da ke kasancewa a gaban mutanen kamfanin Yutong. Mr. Zhu Yongsheng, mai shekaru 28 da haihuwa, wani injiniya ne na kamfanin Yutong, kuma ya halarci dukkan ayyukan cimma kwangilar. Ya ce, "Kasar Amurka ta fi mai da hankali kan karkon bus. Alal misali, tagogin da ke jikin bus. A nan kasar Sin muna yin rufaffun tagogi, amma a kasar Amurka, ana ganin cewa wannan ba shi da kyau. Dole ne za a iya bude wadannan tagogi."

Bayan sun yi kokari a cikin watanni 16 da suka wuce, daga karshe dai, rukunin da ke kula da wannan kwangilar Amurka ya ci nasarar zanen bus dake dacewa da kasuwar Amurka. Amma ba ma kawai kamfanin Yutong yana sayar da bus a kasuwar Amurka ba, har ma yana sayar da bus a duk fadin duniya. A shekara ta 2005, a sau daya kawai ya sayar wa kasar Cuba bus dari 4. A cikin farkon rabin shekara ta 2005, yawan kudin shiga da kamfanin Yutong ya samu daga kasuwannin kasashen waje ya kai dalar Amurka miliyan 37, wato ya ninka sau 7 bisa na makamancin lokaci. Mr. Liu Xiaoming, babban sakataren kungiyar masana'antun kera motoci ta lardin Henan ya ce, dalilin da ya sa kamfanin Yutong ya ci nasara a kasuwannin kasashen duniya shi ne ya fi son yin amfani da fasahohin zamanin yanzu.


1  2  3