Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-03-10 15:52:22    
Hanyar neman bunkasuwa a ketare da kamfanin kera bus kirar Yutong take bi

cri

Assalamu alaikum, jama'a masu karatu, barkanmu da sake saduwa a cikin shirinmu na yau na Bunkasuwar kasar Sin. A watan Disamba na shekara ta 2005, wani jirgin ruwa da ke dauke da wani bus kirar Yutong ya tashi daga tashar ruwa ta Tianjin da ke arewacin kasar Sin zuwa kasar Amurka. Wannan ne karo na farko da aka shigar da bus na kasar Sin a kasuwar kasar Amurka. A shekara ta 2006, za a kara kai sauran bus kirar Yutong 100 zuwa kasuwar kasar Amurka.

Wannan kamfanin da aka fi sani da suna kamfanin kera bus kirar Yutong na Zhengzhou wanda kuma ke sayar da bus a kasar Amurka ba shi da suna a nan kasar Sin yau da shekaru 10 da suka wuce. A wancan lokaci, yawan kamfanonin kera motoci ya kai daruruwa a nan kasar Sin. Lokacin kafuwar kamfanin Yutong, ire-iren bus kirar Yutong da aka kera sun kai 10 da wani abu kawai. Amma kamfanin Yutong ya yi kokari kwarai, yanzu yana sayar da bus da ya kera a kasashe da yankuna kusan 30 ciki har da Rasha da Masar da Iran kuma da Cuba. Daga cikin wadannan kasashe, an fi samun wuyar shiga kasuwar kasar Amurka.

Kowa ya san irin tsauraran ma'aunonin fasahohin bus da kasar Amurka take nema lokacin da ake shigar da bus a cikin kasuwar Amurka. Ya zuwa yanzu dai, kamfanonin kera bus na kasashen Turai da na kasar Japan da kasar Koriya ta kudu kadan ne kawai suka samu izinin shigar da bus nasu a cikin kasuwar Amurka. Kamfanin Yutong ya samu kwangilar shigar da bus a cikin kasuwar Amurka, ba ma kawai yana aiwatar da wata kwangila ba, har ma tana aiwatar da wani babban ayyukan kera bus mai inganci.


1  2  3