Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-03-10 10:44:56    
Dan wasa Liu Xiang yana namijin kokari wajen warkar da jikinsa don shiga manyan   gasannin da za a yi tsakanin kasa da kasa.

cri

Tun dogon lokaci, ba safai akan ga Liu Xiang ya ji rauni ba kodayake ya kan yi horon wasa sosai da shiga gasannin da aka shirya. Wannan ne daya daga cikin kyakkyawan sakamakon da malamin koyarwarsa Mr. Sun Haiping ya samu wajen yin horo. Amma kamar yadda sauran malaman koyarwa suke yi, Mr. Sun Haiping yakan kula da aikin yadda zai daidaita maganar yin horo sosai da rage yawan raunin da watakila 'yan wasa za su samu. Daga baya, Mr. Sun Haiping ya fadi cewa yana nan yana kokarin daidaita wannan magana, ta yadda zai ba da tabbaci ga Liu Xiang don kada ya ji rauni yayin da yake daga matsayin horon wasa. Bugu da kari kuma, Mr. Sun Haiping ya furta, cewa lallai jin raunin da Liu Xiang ya samu ba zato ba tsammani ya ba shi gargadin cewa kowane lamari ba karami ba ne, ya kamata a mai da hankali sosai a kai. Ya ce, Liu Xiang zai ware lokatai da yawa don yin hutu duk bisa burin shiga wasannin motsa jiki na Olympics na shekarar 2008. Amma duk da haka, Liu Xiang zai shiga gasar cin kofin duniya na wasannin guje-guje da tsallae-tsalle da za a yi a watan Agusta a Aden da kuma wasannin motsa jiki na Ashiya da za a yi a watan Disamba na wannan shekara a Doho na kasar Qatar, har da gasannin samun manyan kyaututtuka da hadaddiyar kungiyar wasannin guje-guje da tsalle-tsalle ta duniya za ta shirya a watan Mayu a kasashen Japan da kuma Amurka da dai sauransu.


1  2  3