Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-03-10 10:44:56    
Dan wasa Liu Xiang yana namijin kokari wajen warkar da jikinsa don shiga manyan   gasannin da za a yi tsakanin kasa da kasa.

cri

A matsayin zakara ta wasan tsallake shinge na nisan mita l10 a gun wasannin motsa jiki na Olymipics da aka yi a Aden na kasar Girka, mutane na mai da hankali sosai kan shahararren dan wasa na kasar Sin Liu Xiang. A kwanakin baya ba da dadewa ba, labarin da aka bayar game da raunin da ya yi ba zato ba tsammani yayin da yake yin horon wasan ya jawo hankulan mutane.

Liu Xiang ya yi rauni ne a ran 15 ga watan Fabrairu na bana. Sakamakon haka kuwa ya ga tilas ne ya janye jiki daga gasar wasannin guje-guje da tsalle-tsalle na cikin babban daki na duk kasar Sin ; kuma mutane suna damuwa sosai cewa ko wannan zai jawo mugun tasiri gare shi wajen nuna kwarewa a gasar cin kofin duniya na wasan guje-guje da tsalle-tsalle na cikin babban daki na duniya a shekarar 2006 da za a yi tun daga ran 10 zuwa ran 12 ga wannan wata a Moscow. Amma duk da haka, Liu Xiang bai karaya ba, ya fadi, cewa kodayake ba ya jin dadi lokacin da yake yin gudu, amma bai dakatar da yin horon daga ingancin jikinsa ba ko da na rana guda. Kazalika, ya furta, cewa duk wani abun da zai faru a Moscow, shi kam zai yi namijin kokari wajen nuna kwarewa sosai.


1  2  3