Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-03-08 17:00:46    
kungiyar Hamas ta Palasdinu

cri

Bayan al'amarin da ya auku a ran 11 ga watan Satumba na shekara ta 2001, bi da bi ne Amurka da gamayyar Turai suka shelanta cewa, Hamas kungiya ce ta 'yan ta'adda, kuma suka daskarar da kadarorinta. Daga bisani, Australia ita ma ta yi shelar daskarar da kadarorin kusoshin Hamas.

A cikin 'yan shekarun baya, a yayin da take bayanin rashin yin watsi da gwagwarmaya da makamai, Hamas ta kuma fara daidaita matsayin da ta dauka. A watan Maris na shekara ta 2005, a karo na farko ne kungiyar Hamas ta yi shelar shiga zaben 'yan majalisar dokokin Palasdinu. Shugabannin Hamas sun bayyana cewa, bayan da kungiyar Hamas ta shiga majalisar dokokin Palasdinu da kuma sa hannu cikin tsara manufofi, za ta kara nuna sassauci, haka kuma za ta kara son tuntubar Amurka da dai sauransu da kuma yin shawarwari da su.

Tun bayan da ta kafu, har kullum dai Hamas tana mai da hankali sosai a kan ayyukan jin kai da ba da agaji, sabo da haka, ta samu goyon baya sosai daga wajen jama'ar Palasdinu. A watan Janairu na shekara ta 2006, Hamas ta ci zaben sabbin 'yan majalisar dokoki a yankuna masu cin gashin kansu na Palasdinu.

To, masu sauraro, iyakacin bayanin da muka yi ke nan dangane da kungiyar Hamas. Da haka, ni Lubabatu daga nan sashen Hausa na rediyon kasar Sin da ke nan birnin Beijing ke cewa, assalamu alaikum, ku huta lafiya.(Lubabatu Lei)


1  2  3