Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-03-08 17:00:46    
kungiyar Hamas ta Palasdinu

cri

Jama'a masu sauraro, ni ce Lubabatu ke yi muku assalamu alaikum daga nan sashen hausa na rediyon kasar Sin da ke nan birnin Beijing. Barka da wannan lokaci, kuma barkanmu da sake saduwa da ku a wannan fili namu na amsoshin wasikunku. Tambayar da za mu amsa a wannan mako ta fito ne daga hannun alhaji.Salisu Adamu Rasheed, mazaunin jihar Nassarawa da ke tarayyar Nijeriya. A cikin wasikar da ya aiko mana, ya ce, bayan gaisuwa mai yawa da fatan kuna nan lafiya, ina fatan za ku yi karin bayani dangane da kungiyar Hamas ta Palasdinu, shin ita wace irin kungiya ce? Ban da Alhaji Salisu, wasu masu sauraronmu su ma sun taba yi mana tambayoyin irin wannan, sabo da haka, yanzu sai ku gyara zama ku saurari bayani filla filla a kan kungiyar Hamas ta Palasdinu.

Kungiyar dagiya ta Hamas, wato Hamas a takaice, ta kafu ne a watan Disamba na shekara ta 1987, kuma Ahmed Yassin ne ya kafa ta.

Hamas wadda ke dauke da halin addini da kuma na siyasa, tana nacewa ga murkushe yahudawa masu ra'ayin farfado da kasarsu a yankin Palasdinu ta hanyar nuna karfin tuwo, kuma tana kin zama lafiya da Isra'ila. Tana kuma tsayawa kan kafa wata kasar Palasdinu mai mulkin kanta wadda ke da hedkwatarta a birnin Kudus. Yawan 'yan kungiyar Hamas ya kai sama da dubu 20, haka kuma akwai kungiyoyin dakaru a karkashinta.


1  2  3