Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-03-08 17:00:46    
kungiyar Hamas ta Palasdinu

cri

Bayan da aka kafa kungiyar Hamas, sau da dama ne Hamas ta kai hare-haren kunar bakin wake a kan Isra'ila. A shekara ta 1989, Isra'ila ta mayar da Hamas a matsayin haramtacciyar kungiya, kuma ta kama shugaban addini na Hamas Ahmed Yassin ta tura shi cikin gidan kurkuku.

A shekara ta 1993, bangarorin biyu na Palasdinu da Isra'ila sun kulla sanarwar ka'adoji dangane da cin gashin kan Palasdinu, inda aka amince da Palasdinawa da su fara mulkin kansu a yankin Gaza da Jericho. Amma kungiyar Hamas ta nuna adawa da wannan, kuma ta ci gaba da tsayawa kan gwagwarmaya da Isra'ila ta hanyar nuna karfin tuwo.

Bisa bunkasuwar shirin shimfida zaman lafiya a tsakanin Palasdinu da Isra'ila, Hamas ta taba sauya manufofinta kan gwagwarmaya. A watan Maris na shekara ta 1996, Hamas ta shelanta cewa, za ta yi watsi da nuna karfin tuwo, kuma za ta yi gwagwarmaya ta hanyar siyasa a yankuna masu cin gashin kai. A watan Mayu na wannan shekara, wato 1996, bayan da Benjamin Netanyahu ya hau kan kujerar firaministan Isra'ila, ya dauki tsauraran manufofi a kan batun shimfida zaman lafiya a tsakanin Palasdinu da Isra'ila, har ma an dakatar da shawarwari da ke tsakanin bangarorin biyu a mataki na karshe. Hamas ta kuma yi shelar maido da gwagwarmaya da makamai.

Bayan aukuwar babban rikicin zubar da jini a tsakanin Palasdinu da Isra'ila a watan Satumba na shekara ta 2000, kungiyar Hamas ta kai jerin hare-haren kunar bakin wake a kan Isra'ila. Don ramuwar gayya kuma, Isra'ila ta dauki matakin kisa kai tsaye da kuma manyan ayyukan hare-haren soja a kan Hamas, ta haka, Hamas ta ji rauni mai tsanani. Shugabannin Hamas, ciki har da Ahmed Yassin da magajinsa Abdul Aziz Rantisi, Isra'ila ta yi musu kisan gilla bi da bi.


1  2  3