Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-02-24 14:44:38    
kasar Sin ta sami babban ci gaba a gun wasannin Olympics na lokacin dari

cri

Ko da yake a kan wasu wasanni, kasar Sin ba ta sami lambar zinariya ba, har ma a karo na farko ne kasar Sin ta shiga cikin gasar wadannan wasannin, amma 'yan wasa na kasar Sin sun ba da mamaki. A gun wasannin Olympics na lokacin dari da aka shirya a birnin Torino a bana, a karo na farko, tawagar maza ta kasar Sin ta shiga cikin gasar Snowboard Half-Pipe, haka kuma 'yan wasa biyu wato Sun Zhifeng da Pan Lei ba su sami damar shiga cikin gasa ta zagayen karshe ba, amma kasar Sin ta fara wannan aiki ne cikin shekaru biyu kawai. Shugaban kungiyar Snowboard Half-Pipe Tian Younian ya bayyana cewa,

'A cikin shekaru biyu, mun sami wannan maki, wannan abin yabo ne sosai daga rukunin Snowboard Half-Pipe na duk duniya. A watan Yuni na shekarar da ta gabata, mun je kasashen waje domin horar da 'yan wasammu. Wani mai horar da 'yan wasanni na kasar Canada ya gaya mana cewa, ya taba ganin 'yan wasa masu kyau da yawa, amma kasar Sin tana da 'yan wasa kwararru masu yawan gaske, wannan ya ba shi mamaki sosai.'

Wasan kankara salo-salo ya zama gasar da tawagar kasar Sin ta shiga a shekarar 1980, wato lokacin da kasar Sin ta shiga wasannin Olympics na lokacin dari a karo na farko. A shekarar 1998 a wasannin Olympics na lokacin dari da aka shirya a birnin Nagano, kasar Sin ta sami lambar tagulla, a shekarar 2002 a gun wasannin Olympics na lokacin dari da aka shirya a birnin Salt Lake, kasar Sin ta sami lambar azurfa. A birnin Torino, ko da yake kasar Sin ba ta sami lambar zinariya ba, amma 'yan wasan kasar Sin sun sami na biyu da uku da hudu. Abin da ya burge mu shi ne, ko da yake Zhao Hongbo ya ji rauni kafin watanni shida da aka shirya wasannin a Torino, amma ya shiga cikin wasanni na wannan karo tare da 'yar rakiyarsa Shen Xue. 'Yar wasa Zhang Dan ta ji rauni a yayin da take gasar zagayen karshe, amma ba ta daina ba, ta gama wasanta, haka kuma ta sami lambar azurfa ga kasar Sin. Game da haka, shugaban kwamitin wasannin Olympics na kasar Sin Liu Peng ya ce,

'Abin da ya fi muhimmanci shi ne tawagar kasar Sin ta nuna tsayayyiyar niyya da kasar Sin take da ita, na yi imani cewa, wannan ya fi burge duk duniya idan aka kwatanta shi da lambar zinariya.'(Danladi)


1  2  3