A shekarar 1994, gasar Free Style Aerial Skills ta shiga cikin wasannin Olympics na lokacin dari, 'yar wasa ta kasar Sin mai suna Xu Nannan ta sami lambar azurfa a gun wasannin Olympics na lokacin dari da aka shirya a birnin Nagano a shekarar 1998. A gun wasannin Olympics na lokacin dari da aka shirya a birnin Torino a shekarar da muke ciki, 'yar wasa ta kasar Sin Li Nina ta sake samun lambar azurfa. Ko da yake ba su sami lambar zinariya ba, amma wannan yana da ma'ana sosai. Mataimakin shugaban tawagar kasar Sin Cui Dalin ya bayyana cewa,
'A wannan karo, 'yan wasa na kasar Sin sun sami zama na biyu da na hudu da na shida da na goma, amma wannan ya zama maki mafi kyau da kasar Sin ta samu a tarihi. Ga 'yar wasa mai suna Guo Xinxin, idan ta iya gama karshen sashe na wasanta mafi wuya, to, mai yiwuwa ne za ta sami lambar zinariya.'
1 2 3
|