Jama'a masu karatu, tun daga shekarar 1980 zuwa shekarar 2006, kasar Sin ta riga ta shiga wasannin Olympics na lokacin dari har sau 8, har ma ta sami lambar zinariya a gun wasannin Olympics da aka shirya a birnin Salt Lake a shekarar 2002. A wasannin Olympics da aka shirya a birnin Torino na kasar Italiya a shekarar da muke ciki, kasar Sin ta sami babban ci gaba.
Ko da yake tawagar kasar Sin da ke halartar wasannin Olympics a birnin Torino a bana ba ta sami lambobin zinariya da yawa ba, amma wasu 'yan wasa sun yi bajimta sosai, wannan ya bayyana cewa, kasar Sin ta riga ta sami babban ci gaba a kan wasannin Olympics na lokacin dari.
1 2 3
|