A ran 21 ga wata, ministar kiwon lafiya ta kasar Zambia ta bayyana a gun wani taron majalisar dokoki ta kasar cewa, gwamnatin kasar Zambia ta riga ta kebe kudin da yawansu ya kai dala miliyan 4 da dubu 850 domin shawo kan cutar murar tsuntsaye da mai yiwuwa ne za ta bulla a kasar. Ta ci gaba da cewa, za a yi amfani da wannan kudi ne a kan farfagandar yin rigakafin cutar murar tsuntsaye, ban da wannan kuma, za a bayar da kudin ga mutane da suke kiwon tsuntsayen gida amma aka kashe tsuntsayensu a sakamakon cutar.
A ran 22 ga wata, ma'aikatar kiwon lafiya ta kasar Ukraine ta bayar da wata sanarwar cewa, a 'yan kwanakin baya, tsuntsayen gida masu yawan gaske sun mutu a kauyuka biyu da ke kudancin kasar. A halin yanzu, ana bincike da nazarin tsuntsayen da suka mutu, haka kuma ana kashe kwayoyin cuta a kauyukan biyu.
1 2 3
|