Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-02-23 18:21:41    
Yin rigakafi da shawo kan cutar murar tsuntsaye ya zama muhimmin aiki na kasar da kasa musamman na Afirka

cri

A 'yan kwanakin baya, kungiyar hatsi da aikin gona ta MDD da kasashen Zambia da Rasha da dai sauran kungiyoyin duniya da kasa da kasa suna mayar da yin rigakafi da shawo kan cutar murar tsuntsaye a matsayin muhimmin aiki da ke gabansu.

A ran 22 ga wata, kungiyar hatsi da aikin gona ta MDD ta bayar da wata sanarwa cewa, a halin yanzu dai cutar murar tsuntsaye ta H5N1 tana ci gaba da yaduwa a kasar Nijeriya, idan ba a dauki matakai masu amfani ba, mai yiwuwa ne za a yi hadari mai tsanani a yankin. Sanarwar ta ce, ya kasance da matsaloli biyu a gaban kasar Nijeriya wajen shawo kan cutar murar tsuntsaye: na farko, ba a hana cinikin tsuntsayen gida da aka yi a kasuwa ba; na biyu, ba a gudanar da matakai da gwamantin kasar Nijeriya ta dauka domin kashe tsuntsaye da kiwon lafiya da kyau ba. Ya kamata gwamnatin kasar Nijeriya ta yi wa tsuntsayen gida allurar rigakafin cutar. Amma wannan yana bukatar kudi da yawa, sabo da haka, kamata ya yi kasashen duniya su bayar da taimako ga kasar Nijeriya. Sanarwar ta bayar da shawara ga gwamnatin kasar Nijeriya da ta bayar da isashen kudi ga mutane da suke kiwon tsuntsayen gida da suka kamu da cutar domin sa kaimi gare su da su sanar da halin da cutar take ciki tun da wuri.


1  2  3