To, Malam.Tanimu Abba Mansur, mun dai yi muku takaiataccen bayani a kan jami'ar Beijing, amma muna son yin karin bayani dangane da yadda za a nemi shiga jami'ar tun da kana son neman shiga jami'ar. Lokacin karatu shekaru 4 ne ga masu neman digiri na farko kuma shekaru 2 ko 3 ne ga masu neman digiri na biyu, wato ya danganta ne ga me kake son karantawa. Sa'an nan kuma masu neman digiri na uku su kan shafe shekaru 4 suna karatu. A kowace shekara, akwai zangon karatu biyu, wato na yanayin bazara wanda ya kan fara daga watan Faburairu zuwa watan Yuni da kuma na yanayin kaka wanda ya kan fara daga watan Satumba zuwa watan Janairu mai zuwa.
Daliban kasashen waje suna iya karatu a jami'ar Beijing don neman digiri na farko ko na biyu ko kuma na uku, kuma suna iya karanta Sinanci ko sauran darrusa. Bayan wannan, duk wani dan kasar waje wanda shekarunsa ya kai 18 da haihuwa yana iya neman iznin yin karatu a jami'ar Beijing muddin yana da lafiyar jiki da kuma halin kirki, kuma yana son bin dokokin gwamnatin kasar Sin da na jami'ar da kuma girmama al'adun jama'ar kasar Sin.
To, masu sauraro, karshen bayanin da muka yi dangane da jami'ar Beijing ke nan. Kuna kuma iya karanta cikakken bayani dangane da jami'ar a giza-gizan sadarwa na internet, wato www.pku.edu.cn. Masu sauraro, tilas ne mu sa aya a nan, da haka ni Lubabatu daga nan Beijing ke cewa, sai mako mai zuwa, ku huta lafiya.(Lubabatu Lei) 1 2 3
|