Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-02-22 17:47:34    
Bayani a kan jami'ar Peking

cri

Jami'ar Beijing ita ma ta shahara da shaihunan malamanta masu dimbin yawa da kuma muhallinta mai kyau na yin nazari. A cikin jami'ar, akwai malamai 5,226, daga cikinsu, 1,379 farfesa ne, 1,780 kuma mataimakan farfesa ne. A ko wace shekara, jami'ar ta kan gayyaci mashahuran masana na kasashen duniya da su zo jami'ar don su yi jawabi. A halin yanzu dai, akwai muhimman dakunan bincike 12 na kasa a jami'ar Beijing, sa'an nan kuma, akwai muhimman dakunan bincike 38 a matsayin larduna da cibiyoyin nazarin injiniya na kasa guda biyu. Ban da wannan, akwai kananan asibitoci 8 da kuma asibitocin koyarwa 10 a karkashin jagorancin jami'ar.

Wani abin da ya kamata mu ambata a nan shi ne, dakin karatu na jami'ar Beijing dakin karatu ne da ya fi girma a tsakanin dukannin dakunan karatu na jami'o'in kasashen Asiya, inda ake iya samun littattafai miliyan 5 da dubu 680 da dari 2 da kuma lattattafai dubu 224 wadanda ake iya karantawa a internet. Ban da wannan, jami'ar Beijing kuma tana kan gaba a duk duniya a wajen gina dakin karatu da ake karatu ta injuna masu kwakwalwa.

Jami'ar Beijing tana dora muhimmanci sosai a kan hadin gwiwa da musanya da jami'o'in duniya da hukumomin nazari da kamfanonin kasa da kasa, ya zuwa yanzu dai, ta riga ta kulla huldar mu'amala tsakaninta da jami'o'i fiye da 200 na kasashe da shiyyoyi kusan 50.

A yayin da shugaban kasar Nijeriya Olusegun Obasanjo ke yin ziyara a nan kasar Sin a shekarar bara, wato 2005, ya kuma kai ziyara a jami'ar Beijing, inda aka ba shi digiri na uku na girmamawa.


1  2  3