Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-02-22 17:47:34    
Bayani a kan jami'ar Peking

cri

Jama'a masu sauraro, ni ce Lubabatu ke muku assalamu alaikum daga nan Beijing, barka da wannan lokaci, kuma barkanmu da sake saduwa da ku a wani sabon shirinmu na amsoshin wasikunku. A wannan mako, za mu amsa tambayar da mai sauraronmu Tanimu Abba Mansur ya yi mana a cikin wasikar da ya aiko mana, inda ya ce, ina son zuwa kasar Sin karatu, kuma na ji an ce, jami'ar Beijing tana daya daga cikin jami'o'i masu inganci na kasar Sin, amma ko za ku yi mana takaitaccen bayani a kan jami'ar da kuma yaya zan yi don neman shiga jami'ar tukuna?

Malam. Tanimu, an kafa jami'ar Beijing a shekara ta 1898, wato yau shekaru sama da dari ke nan da aka kafa ta. Ita jami'a ce ta farko wadda ke koyar da kome da kome ta kasar Sin. A halin yanzu dai, akwai tsangayoyi da sassa da yawansu ya kai 47 a cikin jami'ar, haka kuma akwai fannoni 101 da ake kwarewa a kai ga dalibai masu neman digiri na farko da kuma 224 ga masu neman digiri na biyu da kuma 202 ga masu neman digiri na uku. A yayin da take ci gaba da rike matsayi mai rinjaye a wasu fannonin gargajiya, jami'ar Beijing ta samu babban ci gaba a wajen wasu darrusa na musamman.

Bisa kidayar da aka yi a watan Oktoba na shekara ta 2004, akwai dalibai 14,486 a jami'ar Beijing wadanda ke neman digiri na farko, sa'an nan kuma, akwai 9,004 wadanda ke neman digiri na biyu, bayan haka kuma, akwai masu neman digiri na uku 4,759. Akwai kuma dalibai sama da 4000 daga kasashe 80 wadanda ke karatu na dogon lokaci ko gajere a cikin jami'ar.


1  2  3