Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-02-13 15:49:00    
Kasar Sin ta bayar da rahoto kan halin da take ciki a fannin ciwon AIDS

cri

Rahoton da aka bayar a ran 25 ga wata ya yi nuni da cewa, an kara samun Sinawa masu dauke da kwayoyin cutar AIDS kimanin dubu 70 a shekarar 2005, halayen musamman da kasar Sin take da su a fannin cutar AIDS su ne, da farko, an samu wannan cuta a wurare daban daban a kasar Sin; na biyu kuma, shan miyagun kwayoyi da kuma yin jima'i sun zama manyan hanyoyin yaduwar cutar AIDS; na uku, masu cutar suna bakin mutuwa; na hudu, an kara yada wannan cuta tsakanin mutane, al'ummar kasar ba su da isasshen ilmi game da cutar AIDS, don haka ya kasance da barazanar yaduwar wannan cuta.

Masana daga hukummomin UNAIDS da WHO sun sa hannu cikin wannan aikin kimantawa, sun kuma amince da wannan aiki sosai. Wakilin hukumar UNAIDS da ke kasar Sin Mr. Joel Rehnstrom ya bayyana cewa, hukummomin UNAIDS da WHO suna ganin cewa, kasar Sin tana tafiyar da aikin kimantawa yadda ya kamata, kuma adadin da ta samu yana iya wakiltar halin da kasar Sin take ciki a fannin cutar AIDS. Suna darajanta gwamnatin kasar Sin saboda ta kyautata tsarin sa ido cikin himma da kwazo, don shawo kan kalubalen da cutar AIDS ke jawowa. Ko a yanzu ko a nan gaba, hukummomin UNAIDS da WHO suna goyon bayan gwamnatin kasar Sin kamar yadda suka yi a da wajen kara sa ido kan wannan mummunan cuta da dai sauransu.


1  2  3