Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-02-13 15:49:00    
Kasar Sin ta bayar da rahoto kan halin da take ciki a fannin ciwon AIDS

cri
Ran 25 ga watan Janairu, ma'aikatar kiwon lafiya ta kasar Sin ta hada kai da Hukumar Cutar AIDS ta Majalisar Dinkin Duniya wato UNAIDS da kuma Kungiyar Kiwon Lafiya ta Duniya wato WHO sun bayar da wani rahoto dangane da halin da kasar Sin take ciki wajen cutar AIDS da kuma ayyukan shawo kanta a shekarar 2005. Rahoton ya yi bayanin cewa, har zuwa karshen shekarar 2005 da ta gabata, akwai masu dauke da kwayoyin cutar AIDS kimanin dubu 650 a kasar Sin, a ciki har da masu cutar AIDS kimanin dubu 75. Rahoton ya yi nuni da cewa, har yanzu yawan masu cutar yana ta karuwa, don haka ya kasance da barazanar yaduwar wannan cuta.

Adadin baya bayan nan da aka bayar a ran 25 ga watan jiya ya nuna cewa, yawan mutanen da ke dauke da cutar AIDS ya ragu da dubu 190 bisa na shekara ta 2003. Manyan dalilan da suka sa haka su ne saboda a cikin binciken da aka yi a shekarar 2003, an kiyasta cewa, mutanen da suka kamu da kwayoyin cutar AIDS ta hanyoyin bayar da jini tare da karbar kudi da kuma yin jima'i tsakanin maza suna da yawa, amma a zahiri kuma, ba su da yawa sosai. Mataimakin ministan kiwon lafiya na kasar Sin Mr. Wang Longde ya bayyana cewa, kasar Sin ta kara sa ido kan mutanen da aka ambata tun farko a cikin shekaru 2 da suka gabata, sa'an nan an habaka sa ido kan mutane, kungyoyi da hukummomin da ke kula da ayyukan kimantawa sun tafiyar da ayyukansu cikin tsanaki.

Mr. Wang ya kara da cewa, a cikin shekarar 2004 da ta gabata, kasar Sin ta yi binciken mutanen da suka bayar da jini tare da karbar kudi, ta haka an gano yawan masu dauke da kwayoyin cutar AIDS daga cikin wadannan mutane. An kuma shawo kan wannan cuta a tsakanin 'yan ludu da 'yan madigo, a sakamakon haka an gano halin da wadannan mutane suke ciki a fannin cutar AIDS.


1  2  3