Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-02-10 16:45:23    
Bikin sinima a birnin Sanya

cri

An yi manyan gyare-gyare a kan lambar yabo mai suna zakarar zinariya da aka bayar a shekarar 2005, wato a karo na farko sinimar da aka dauka cikin hadin guiwar babban yankin kasar Sin da Hongkong da Macao da Taiwan za su iya samun lambar yabo mai suna zakarar zinariya. Wani mashahurin dan wasan sinima ne mai suna Cheng Long shi ma ya sami lambar nan, ya yi murmushi da bayyana cewa, a da, ban taba samun lambar nan ba, duk saboda masu ba da sharhi sun tabbatar da 'yan wasa a fanni ne na nuna fasahohin wasanni , amma ina mai da muhimmanci sosai ga yadda nake yin wasan sinima, ba wajen nuna fasahohin wasanni ba, yanzu ni ne dan wasan sinima, shi ya sa ina son in bayyana cewa, ni ne dan wasan sinima da ke iya bayyana fasahohin wasannin sinima.

Sinimar kasar Sin da ke da shekaru 100 a tarihin kasar Sin , ta taba samun wadatuwa, amma ta taba shiga halin kaka-ni-ka-yi a cikin 'yan shekarun nan da suka wuce. Bayan kokarin da masu aikin sinima suka yi cikin himma da kwazo ne, a cikin 'yan shekaru biyu da suka wuce, ta kara ba da tasiri ga kasa da kasa a kowace rana. Wato ta sami alamar sake farfadowa. (Halima)


1  2  3