Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-02-10 16:45:23    
Bikin sinima a birnin Sanya

cri

Abin da kuka ji shi ne faye-fayen da muka sanya muku dangane da sinimar da ake kira " Kekesili"

Sinimar "Kekesili" da sinimar " kan tsaunukan Taihang" sun sami lambar yabo mai suna zakarar zinariya. Sinimar "Kekesili" an dauke ta ne bisa wani hakikanin labarin da aka samu, wannan ne sinimar farko da ta bayyana kundunbalar da aka yi a yammacin kasar Sin. Babban mai ba da jagoranci ga wasannin sinimar shi ne wani saurayi mai suna Lu Chuan. Shi da 'yan kungiyarsa sun dauki sinimar nan mai burge 'yan kallo sosai da sosai a yankin kiyaye halittu na Kekesili da ke kan manyan tsaunuka masu fadi na Tibet da Qinghai wadanda suke da nisan mita dubu 5 daga leburin teku.

Sinimar ta bayyana masu aikin sintiri a tsaunuka guda 8 da suka shiga wurin "Kekesili" don hana kashewar da aka yi wa gargadan Tibet, wadannan mutane sun sha wahaloli da yawa, sa'anan kuma an rage sauransu guda biyu kawai, sinimar ta sami lambobin yabo da yawa da kudadden takardun kallo da yawa daga gida da waje.

A cikin 'yan shekarun nan da suka wuce, samari masu aikin daukar sinima sun dauki sinima da yawa da suka sami karbuwa daga wajen 'yan kallo. Daga cikinsu da akwai wata mai ba da jagoranci ga wasannin sinima Ma Liwen wadda ta sami lambar yabo mai suna zakarar zinariya . ta bayyana cewa, lokacin da na soma daukar sinima, da wuya zan sami kudadde da yawa. Da na dauki sinimar farko, kudadde kadan ne kawai na samu, amma na yi ta daukar sinima har cikin shekara da shekaru, a ganina, dole ne na yi aikin daukar sinima a kai a kai da kuma daukar sinimar da ke da batun da na fahimta sosai.


1  2  3