Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-02-08 17:59:21    
Bayani a kan birnin Beijing

cri

Beijing tsohon birnin ne na kasar Sin wanda ya shahara a fannin tarihi da na al'adu. Birnin Beijing yana da tsawon tarihi har na shekaru fiye da dubu 3, kuma tun daga da da da can, ita muhimmin birni ne na arewacin kasar Sin a fannin aikin soja da kuma sufuri. A ran 1 ga watan Oktoba na shekara ta 1949, an yi kasaitaccen bikin kafa jamhuriyar jama'ar kasar Sin a filin Tian'anmen na birnin Beijing, to, tun daga nan, Beijing ya zama sabuwar hedkwatar kasa Sin da kuma cibiyar kasar Sin ta siyasa da al'adu da kuma yin cudanya da kasashen waje. Yanzu, da akwai jami'o'i 66 da hukumomin nazari sama da 500 a birnin Beijing.

Tun bayan da aka kafa jamhuriyar jama'ar kasar Sin, tattalin arzikin Beijing yana bunkasa cikin sauri. An kafa masana'antu iri iri a nan Beijing, ciki har da masana'antar harhada magunguna da ta kayan lantarki da kayan saka da dai sauransu. Ban da wannan kuma, a cikin 'yan shekarun nan, harkokin yawon shakatawa da kasuwanci da kudi da samar da labarai da dai sauransu su ma sun sami saurin bunkasuwa a nan birnin Beijing, kuma Beijing ya riga ya zama daya daga cikin manyan kasuwanni da tashoshin kwastan na kasar Sin. Muhimman hajjojin da yake fitarwa zuwa kasashen waje su ne kayan saka da tufafi da kayayyakin fasaha da magungunan sha da injuna da kayayyakin lantarki da amfanin gona da dai sauransu. Beijing babbar mahadar hanyoyin dogo ne da na jiragen sama ta kasar Sin, yawan hanyoyinsa ya kai kilomita 0.54 a ko wane muraba'in kilomita, har ma Beijing ya kai matsayi na farko a wannan fanni a duk fadin kasar Sin.


1  2  3