Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-02-08 17:59:21    
Bayani a kan birnin Beijing

cri

Assalamu alailum, jama'a masu sauraronmu, barkanmu da sake saduwa a wani sabon shirinmu na amsoshin wasikunku, wato shiri ne da ke amsa tambayoyin masu sauraronmu. A cikin shirinmu na yau, ni Lubabatu zan ja ragamar wannan shiri, inda zan amsa tambayar da Malam.Shekarau Mustafa daga birnin Kebbi na tarayyar Nijeriya ya yi mana, inda ya ce, bayan gaisuwa mai yawa da fatan kuna nan lafiya, ina so ku yi mana dan bayani a kan birnin Beijing, babban birnin kasar Sin.

To, Malam shekarau, Beijing babban birni ne na jamhuriyar jama'ar kasar Sin, kuma tana arewacin kasar Sin. A halin yanzu dai, akwai manyan unguwanni 10 da gundumomi 8 a birnin Beijing. Beijing yana karkashin mulkin gwamnatin tsakiya na kasar Sin kai tsaye, kuma na daya daga cikin biranen kasar Sin da suke bude kofa ga kasashen waje. Fadin birnin Beijing ya kai muraba'in kilomita dubu 16 da dari 8, kuma yawan mutanensa ya kai miliyan 12 da dubu 510. 'yan kabilar Han da Hui da Man da Mongoliya da dai sauransu suna zaune a birnin Beijing.


1  2  3