Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-02-07 17:14:34    
An yi yawon shakatawa a hotel irin na kabilar Zang a Tibeti na kasar Sin

cri

Ban da wannan kuma, a karamin hotel na Balangxue, 'yan yawon shakatawa suna iya samun sauki wajen musanyar ra'ayoyinsu. Mutane da suka zo daga wuraren daban daban na duk duniya sun zauna a hotel din, sun bayyana abubuwa na farin jiki da bakin jiki da ke faruwa a kan tafiyarsu; ko da yake suna da al'au irin daban daban, amma suna iya fahimtar juna da kyau.

A tsakiyar hotel din, an kebe wani wuri da aka dasa furanni, a yammacin wurin, sai wani fili ne da ake shan ti, inda 'yan yawon shakatawa suke iya sha ti ko cin abici ko kallon littattafai ko yin tadi.

Wani 'dan yawon shakatawa da ya zo daga lardin Sichuan na kasar Sin Malam Zhang Shukai ya gaya wa wakilinmu cewa, a ko wace rana, wannan fili yake cike da mutane. Ta ce haka,

'A kullum mutane daban daban na gida da na waje suna zama a tohel na Balangxue, dukkansu 'yan yawon shakatawa ne. a wani lokaci, mutane 20 ko fiye suna zauna a filin, suna tunani, babu wanda ya yi magana ko kadan. A wannan fili, kana iya samun abokai da yawa. Haka kuma a hotel na Balangxue, kana iya kwantar da hankalinka, kana iya waiwaiyo baya. Wannan abin da nake ji a rai yana da kyau. Sabo da haka, ina son hotel na Balangxue, ina kaunar Lasa.'(Danladi).


1  2  3