Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-02-07 17:14:34    
An yi yawon shakatawa a hotel irin na kabilar Zang a Tibeti na kasar Sin

cri

Game da 'yan yawon shakatawa da yawa da ke ziyarar birnin Lasa, ban da kyakkyawan sararin sama da kogin ruwa mai tsabta da gidajen ibada na Lama, wuraren da suka fi son ziyara su ne kananan hotel irin na kabilar Zang a Tibeti. Lasa birni ne mai cike da hasken rana. A wata rana da yawa, wakilinmu ya fita daga titin Bakuo da ke dab da gidan ibada na Dazhao, sai ya sa kafa a kan gabashin hanyar Beijing, sabo da hotel mai suna Balangxue da zai tafi yake dab da hanyar.

Shigarsa ke da wuya, sai ya ga wata yarinya tana rajista, wadda take ado kamar wata 'yar yawon shakatawa. Wannan yarinya ta gaya wa wakilinmu cewa, sunanta Li Biqian, wata 'yar yawon shakatawa da ta zo daga jihar Guangdong da ke kudancin kasar Sin. Kafin ta zo Tibeti, ta sami labarai da yawa daga Internet game da yawon shakatawa a Tibeti, ta yadda ta san cewa, hotel na Balangxue wani wuri mai kyau domin zauna. Ta ce haka,

'A kan internet, mutane da yawa suna bayar da shawarar yin yawon shakatawa a hotel din. Sabo da ya yi araha, amma abu na muhimmanci shi ne salonsa ya kasance da na kabilar Zang, ina sha'awar wannan salo sosai. shi ya sa na zo nan, kuma ina jin dadin wannan tafiya.'


1  2  3