Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-02-07 17:14:34    
An yi yawon shakatawa a hotel irin na kabilar Zang a Tibeti na kasar Sin

cri

Ban da hotel na Balangxue kuma, birnin Lasa yana da irin wannan hotel na kabilar Zang fiye da goma, a halin yanzu dai suna jawo hankulan 'yan yawon shakatawa da yawa daga kasar Sin da kasashen waje. Ko da yake irin wannan hotel sun yi araha, amma suna da abubuwa na musamman da dama.

A cikin hotel na Balangxue, akwai wani allon ba da labari game da hayar mota da sayar da kayayyaki da neman abokai domin yin yawon shakatawa tare da dai sauransu. A 'yan kwanakin baya, wata 'yar yawon shakatawa mai suna Zhong Yingxin ta bayar da wani labarin neman abokan yin yawon shakatawa tare. Ta ce haka,

'Ni ba na so in bi kamfanonin shirya yawon shakatawa ko kadan, sabo da babu 'yanci. Shi ya sa na bayar da labari a kan allon, ina son neman mutane biyu, mu yi yawon shakatawa tare.'

Zhong Yingxin taci gaba da cewa, sabo da wannan allo, mutane da yawa sun riga sun tumtube ta. Amma ta yanke shawarar tafiya tare da 'yan mata biyu da suka zo daga birnin Shenzhen.


1  2  3