
Ban da ma'adinan zinariya kuma akwai filayen lu'u-lu'u masu daraja sosai, filayen ma'adinan li'u-lu'u suna da fadi sosai. A wuraren nan kuma masu shakatawa na duniya su iya kai ziyara a filayen nan, kuma su iya saye kayayyakin zinariya da aka yi.
Ban da haka kuma, a kasar Afrika ta kudu akwai shiyoyyin dabobbin daji, irinsu kamar damisa da giwa da shannu da sauran ire irensu. Masu shakatawa su iya dau mota don neman kallo dabobbin daji iri iri.(Dije) 1 2 3
|