
A kasar Afrika ta kudu akwai shiyoyyin kiyaye dabobbin daji da yawa, kuma akwai manyan hotel hotel da wurare masu ni'ama da yawa kuma akwai gabobbin teku masu kyau. A kasar Afrika ta kudu, an iya dau mota don yin shaktawa a duk fadin kasar nan. Ban da wuraren halitta masu ni'ima,kuma akwai manyan dakunan yin ba je koli da na nuna fasaha da na wasan motsa jiki, kuma akwai dakunan dafa abinci iri iri da dakunan nuna sinima da dakunan nuna wasan opera iri iri, wato a dukkan wuraren da kake so yin nishadi, sai za ka iya morewa jin dadi sosai.
Birnin Cape Town shahararren birni ne dake kudancin kasar Afrika ta kudu, Wannan shi ne birni mafi tsoho a kasar Afrika ta kudu, kuma shi ne wani dutse mai daraja sosai a duk Nahiyar Afrika, wadnnan wurare masu ni'ima sosai. A nan kuma akwai tashoshin ruwan teku da kauyeun masu kama kifaye. Kuma ga gadun noman innabi, ga gabobbin ruwan teku masu kyau.A karkarar birnin Cape Town, akwai wani babban tudu shi ne abin shaida ga wannan birni.
1 2 3
|