Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-01-19 16:35:56    
An tara kudaden da yawansu ya kai dallar Amurka biliyan 1.9 don yaki da cutar murar tsuntsaye

cri

A matsayinta na daya daga cikin masu shirya taron, kasar Sin ita ma ta amince da bayar da dallar Amurka miliyan 10. Firayin ministan kasar Sin Wen Jiabao ya kuma bayar da shawarwari hudu dangane da kara ingiza hadin gwiwa tsakanin kasa da kasa a wajen yaki da cutar murar tsuntsaye. Wato na farko, a kafa tsarin hadin gwiwa tsakanin kasa da kasa kan yaki da cutar. Na biyu kuma a inganta karfin yaki da cutar. Na uku, kamata ya yi majalisar dinkin duniya da kungiyoyin duniya da abin ya shafa sun ba da taimakonsu kamar yadda ya kamata. Na hudu, a kara neman samun kudin tallafawa. Ban da wannan, ya kuma bayyana cewa, kasar Sin za ta ci gaba da shiga cikin hadin gwiwa tsakanin kasashen duniya a wajen yaki da cutar murar tsuntsaye, kuma za ta kara bayyana halin da take ciki a fannin yaki da cututtuka da kuma ayyukan da take yi a fili. Ya ce, 'kasar Sin kasa ce mai daukar alhakinta, tana son ci gaba da sa hannu cikin hadin gwiwar kasa da kasa a kan yaki da cutar, kuma za ta yi musayar fasahohi na magance cutar tare da kasashen da abin ya shafa, kuma za ta ba da taimako a wajen tsara matakan yaki da cutar.' (Lubabatu Lei)


1  2  3