Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-01-19 16:35:56    
An tara kudaden da yawansu ya kai dallar Amurka biliyan 1.9 don yaki da cutar murar tsuntsaye

cri

A ran 18 ga wata, an rufe taron kasa da kasa kan tara kudade domin yaki da cutar murar tsuntsaye wanda aka shafe kwanaki biyu ana yinsa a nan birnin Beijing, kuma gaba daye ne aka tara kudaden da yawansu ya kai dallar Amurka biliyan daya da miliyan 900. Wannan ya zarce yawan gibin kudi da bankin duniya ya tantance a wajen yaki da cutar kwarai da gaske. Za a yi amfani da kudaden nan a wajen taimaka wa kasashen da ba su samun kudin shiga sosai a wajen yaki da cutar murar tsuntsaye a shekaru uku masu zuwa, don hana ci gaban yaduwar cutar murar tsuntsaye da kuma magance yaduwarta a tsakanin 'yan Adam.

Da ma bankin duniya da dai sauran kungiyoyin duniya sun kimanta cewa, ya kasance da gibin kudi da yawansa ya kai dallar Amurka kimanin biliyan daya da miliyan 200 zuwa biliyan daya da miliyan 400 a wajen yaki da cutar murar tsuntsaye a duk fadin duniya. Sabo da haka, masu shirya taron nan na kasa da kasa a kan tara kudaden yaki da cutar murar tsuntsaye suna son samun wadannan kudade a kalla a gun taron. A gun taron manema labaru da aka shirya bayan da aka rufe taron nan na tara kudi a ran 18 ga wata, wakilin kwamitin gamayyar Turai Markos Kyprianou ya bayyana cewa, an cimma cikakkiyar nasara wajen cike gibin da ke kasancewa a wajen samun kudaden yaki da cutar murar tsuntsaye. Ya ce, 'An tara kudaden da yawansu ya kai dallar Amurka biliyan daya da miliyan 900 a gun wannan taro, ya kamata mu ji alfahari domin mun ci nasara. Daga cikin kudaden, akwai dallar Amurka kusan biliyan daya da aka bayar da su kamar kyauta, wannan yana da muhimmanci, sabo da shi abu ne da kasashe masu tasowa ke tsananin bukata. Sauran miliyan 900 kuma kudi ne na rance, wadanda za a yi amfani da su wajen kyautata manyan ayyuka na kasashen da abin ya shafa.


1  2  3