Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-01-19 16:35:56    
An tara kudaden da yawansu ya kai dallar Amurka biliyan 1.9 don yaki da cutar murar tsuntsaye

cri

 

Kasashe da yankuna masu sukuni da kuma wasu kungiyoyin duniya su ne suka fi bayar da kudade a gun taron nan. Gaba daya ne kwamitin gamayyar Turai da kasashenta sun amince da bayar da kudin da yawansu ya kai dallar Amurka miliyan 250, kuma Amurka ta amince da bayar da miliyan 334. Ban da wannan, bankin duniya ya bayar da rancen kudin da yawansa ya kai dallar Amurka miliyan 500. Yawan kudaden da bankin raya Asiya da Japan ko wanensu ya bayar shi ma ya wuce dallar Amurka sama da miliyan 100.

An ce, za a kashe yawancin kudaden da aka tara a gun taron a wajen taimaka wa yankunan da suka fi shan wahalar cutar murar tsuntsaye, wato yankuan gabashin Asiya da kudu maso gabashinta da kuma Afirka wadda ke fuskantar babban hadarin samun yaduwar cutar. Wani jami'in ma'aikatar kiwon lafiya ta kasar Indonesia Umar Fahmi ya gaya wa manema labaru cewa, kasar Indonesia za ta kashe kudin taimako da ta samu a wajen fadakar da jama'a a kan yaki da cutar murar tsuntsaye. Ya ce, 'za mu yi amfani da kudaden a wajen horar da masu aikin sa kai da yawa a kauyuka, don su wanzar da ilmin rigakafin cutar murar tsuntsaye gida bayan gida. Bayan haka kuma, za su sanar da hukumomin kiwon lafiya na wurin a kan labaran cutar tun da wuri, ta yadda za mu kyautata tsarin ba da gangami.'


1  2  3