|

An bayyana cewa, Hua Tuo ya yi nazari sosai kan ciwon da aka kamu da shi bisa sanadiyar kwarkwata da dai sauran irinsu.
Sa'anan kuma, Hua Tuo ya yi nazari sosai kan ciwon da a kan kamu da shi wajen tunani da ciwace-ciwace da tsofaffi su kan kamu da su.
A duk rayuwarsa, Hua Tuo ya yi aikin likitanci sosai, ya tafi wurare da yawa don kawar da wahalolin da jama'ar farar hula suke sha bisa sanadiyar fama da ciwace-ciwace, mutane suna nuna yabo gare shi daga zuri'a zuwa zuri'a, lardin Anhui da lardin Shandong da lardin Jiangsu na kasar Sin su ne muhimman wuraren da Hua Tuo ya yi aikin likitanci, ya zuwa yanzu, akwai kasancewar haikalin tunawa da Hua Tuo a wadannan wurare. Amma kalmomin da aka yi da cewar wai Hua Tuo ya sake rayuwa a duniya sun zama babban yabo da aka yi ga likitoci na yanzu. (Halima) 1 2 3
|