Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2005-12-28 16:04:16    
Wani mutumin kasar Sin na zamanin da mai suna Hua Tuo

cri

Dayake ya yi amfani da maganin hana jin zafin ciwo mai suna "Mafeisan" , shi ya sa Hua Tuo ya kara kyautata aikinsa wajen tiyata, har ma ya kan warkar da sauran ciwace-ciwace da aka kamu a cikin ciki ta hanyar aikin tiyata. Ana yaduwa da cewa, a wata rana, wani mutum yana zogi a ciki sosai da sosai, bayan da Hua Tuo ya yi masa dudduba, sai ya yanke da cewa, ciwonsa ciwo ne da ake kira "Appendicitis" cikin Turanci , ya sha masa maganin hana jin zafi mai suna "Mafeisan", sa'anan kuma ya yi masa tiyata, ya cire masa wurin ciwo da ke rubewa, sa'anan kuma ya dinke wurin da aka yi tiyata, kuma ya shafa wa wurin tiyata da maganin da ya hada, ba da dadewa ba wanda ya kamu da ciwon nan ya sami warkewa.

Hua Tuo yana daya daga cikin wadanda suka soma aikin likitanci ta hanyar motsa jiki. A ganinsa, ya kamata kowane mutum ya motsa jikinsa don kara koshin lafiya, ta hakan, to tabbas ne za a sami sakamakon yin rigakafin kamuwar ciwace-ciwace da ba da taimako ga warkar da su.


1  2  3