Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2005-12-28 16:04:16    
Wani mutumin kasar Sin na zamanin da mai suna Hua Tuo

cri

A kasar Sin, in ana son bayyana wani likitan da ke da fasahohi sosai, sai a kan ce, shi ne tamkar yadda Hua Tuo ya sake rayuwa a duniya. Hua Tuo din nan shi ne wani mashahurin likita na zamanin da na kasar Sin.

An haife Hua Tuo a karni na biyu zuwa na uku na karshen daular Han ta Gabas , kuma shi mutumin lardin Anhui na gabashin kasar Sin na yanzu ne. Tun lokacin da ya ke karami, ya yi kokarin karatu, musamman ma ya yi kishin nazarin dabarun aiwatar da aikin likitanci da na kiwon lafiya, ya yi ta tafiya a ko'ina don ziyartar shahararrun likitoci. A zamanin da yake rayuwa, daular Han ta gabas da ke mulkin dauloli daban daban ba ta da karfi, tamkar yadda ba a kafa ta ba, ana ta yin rikicin neman kafa daular tasku a tsakanin dauloli daban daban, Hua Tuo ya nuna tausayi sosai ga farar hula da suke fama da ciwace-ciwace, shi ya sa ya yi niyyar ba da taimako ga jama'a farar hula ta hanyar likitanci. Ya yi nazari kan ilmin likitanci sosai, ba ma kawai ya yi koyi daga wajen shahararrun likitoci ba, hatta ma ya tattara da kuma koyi fasahohin da aka dandana wajen warkar da marasa lafiya ta hanyar yin amfani da dabarun gargajiyar kasar Sin, a kai a kai ne ya sami ilmin likitanci da yawa. Ya kware wajen warkar da marasa lafiya na fannoni daban daban, musamman ma ya kware wajen aikin tiyata, shi ya sa ake kiran shi da cewa " Kakanin kakanin masu aikin tiyata"

Da farko ya kago wani maganin hana jin zafin ciwo da a kan yin amfani da shi wajen aikin tiyata, maganin nan da aka hada shi ta hanyar yin amfani da wani tsire mai suna "datura" cikin turanci, tamkar yadda giyar magani take, ana kiran maganin nan da sunan "Mafeisan".


1  2  3