Idan an tabo magana a kan masu gida na wadannan gine-gine wato tsakar gida, to, ko shakka babu za a yi magana a kan shahararrun 'yan kasuwa na lardin Shanxi na kasar Sin. Bisa ci gaban da aka samu wajen bunkasa harkokin kasuwanci bayan karni na 18, 'yan kasuwa sun gano cewa, an yi ta gamuwa da wahalhalu wajen jigilar kudaden karfe cikin kwanciyar hankali. Da ganin haka, 'yan garin Pingyao wadanda suka kware wajen gudanar da harkokin kasuwanci, sun kago wata irin takardar kudi ta gargajiyar Sin. A shekarar 1824, an gina banki mai zaman kansa na farko na gargajiyar Sin a birnin Pingyao. Daga nan ne 'yan kasuwa sun fara ajiye kudi da daukar kudi a irin wannan banki da sauki.
Ko da yake yanzu an riga an soke duk irin wannan banki, amma bayan da Hamasita Takesi, shehun malami da ke aiki a Jami'ar Tokyo ta Japan ya ziyarci dakin nunin tsoffin takardun kudi na gargajiyar Sin a birnin Pingyao, ya bayyana cewa, "sashen nazarin al'adun gabashin Asiya na Jami'ar Tokyo yana da wasu littattafan tsoffin takardun kudi na lardin Shanxi. Daga cinciki da muka yi, mun gano cewa, a can zamanin da, 'yan kasuwa na lardin nan ba ma kawai sun gudanar da harkokinsu a kasar Sin ba, har ma sun gudanar da harkokinsu a kasashen waje kamar kasashen Asiya musammam ma kasashen gabashin Asiya.
To, jama'a masu sauraro. Karshen shirinmu na yau na yawon shaktawa a kasar Sin ke nan daga sashen Hausa na rediyo kasar Sin da ke nan birnin Beijing. Halilu ne ya fassara kuma ya karanto muku, sai mun ce, assalamu alaikunm. (Halilu) 1 2 3
|