Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2005-12-27 16:00:51    
Tsohon gari da ake kira Pingyao a kasar Sin

cri

Daga siffar garin nan, an gano cewa, a zamanin da, Sinawa sun taba nuna girmamawa sosai ga kunkuru. A ganin Sinawa, kunkuru alamar tsawon rai ne. Dalilin da ya sa siffar garin Pingyao ta yi kamar Kunkuru shi ne domin ana fatan garin nan zai riku kulla yaumin.

Ban da wannan kuma an yi gine-gine masu ban sha'awa a tsohon garin Pingyao. Yawan gine-gine irin na tsakar gida da aka yi a cikin tsohon garin ya wuce 3700, daga cikinsu akwai 400 da 'yan doriya wadanda suke nan sumul garau. Da budurwa Li Yu, 'yar yawon shakatawa ta tabo magana a kan wadannan gine-gine, sai ta ce, "ya zuwa yanzu dai, wadannan gine-gine irin na gargajiyar kasar Sin suna nan sumul garau, ba a canja su ba, daga wajensu na iya gano irin wadatuwa da aka taba yi a garin Pingyao a zamanin da. Yayin da na sa kafa a cikin garin, sai na nutse cikin kogin tunani, na yi kamar ina komawa zamanin da a garin."


1  2  3