Daga cikin kananan garuruwa da yawansu ya wuce dubu 10 a kasar Sin, akwai wani karamin gari da ake kira Pingyao cikin Sinanci, wanda kuma ba safai a kan iya samun irinsa ba a kasar. A halin yanzu, garin Pingyao yana daya daga cikin tsoffin garuruwa na kasar Sin wadanda aka kare tsoffin gine-gine masu sigogin musamman na zamanin daular Ming da ta Qing wato bayan karni na 14. Da yake tsohon garin Pingyao yana nan sumul garau, kuma ba a canja shi ba, sai an shigar da shi cikin sunayen tsoffafin kayayyakin al'adu na duniya da sauki.
Garin Pingyao yana lardin Shanxi da ke tsakiyar kasar Sin, yau shekarunsa sama da 2,700 da ginawa. Tun da aka gina shi, garin ya sha samun manyan sauye-sauye a zamanin da, gari na yanzu gari ne da aka sabunta a zamanin daular Ming da ta Qing.
Tsohuwar ganuwa ta garin pingyao wanda tsawonsa ya zarce mita 6000, tsayinsa kuma mita 12 ne, ta kasa garin nan kashi biyu wato tsohon gari da sabon gari. Ba a canja tsohon gari ko kadan ba, sabon gari kuma iri na zamani ne. Budurwa Liang Yuru, jagorar yawon shakatawa ta garin ta bayyana cewa, idan an hangi garin Pingyao daga sararin sama, to, za a yi mamaki da ganin cewa, siffar tsohon garin Pingyao ta yi kamar wani babban kunkuru. Ta ce, "kofar kudu ta tsohon garin Pingyao ta yi kamar kan kunkuru, rijiyoyi biyu da ke bakin kofar sun yi kamar idanunsa biyu na kunkurun, kofar arewa wutsiyarsa ne, haka nan kuma ya kasance da garuruwa 'yan kalilan guda hudu wadanda ke fuskantar juna a waje da garin, sigoginsu sun yi kamar akaifu hudu na kunkurun wadanda a bude suke."
1 2 3
|