Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2005-12-08 17:20:04    
Kimiyyar nanometre ta kasar Sin

cri

Ban da wannan kuma cibiyar binciken kimiyyar Nanometre ta kasar Sin ta gina dakunan yin gwaje-gyaje guda 6 a jami'ar Beijing da ta Qinghua da ofishin yanayin halittu da na kimiyyar binciken sinadari na cibiyar binciken kimiyya ta kasar Sin domin ba da taimako wajen yin bincike.

Bayan da cibiyar binciken kimiyyar Nanometre ta kasar Sin ta dauki ma'aikatanta ta hanyar ba da sanarwa har sau 14, yawan mutane masu zurfin ilmi da take da su yanzu ya kai 36. Daga shekarar 2004 zuwa ta 2005, jimlar kudin da cibiyar ta samu daga kasashen waje domin tafiyar da aikinta ta kai Renminbi fiye da Yuan miliyan 31. Har zuwa yanzu yawan bayanonin da masu yin bincike na cibiyar suka bayar cikin muhimman mujallolin kasashen duniya ya kai 14, wato an riga an samu karfin yin binciken kimiyya bisa mataki na farko.

Ana ta yin gine-gine, sa'an nan kuma ana tafiyar da aikin yin bincike,cikin shekara daya da 'yan watannin da suka wuce, cibiyar binciken kimiyyar Nanometre ta kasar Sin wadda take tafiyar da sabon tsarin aiki tana nan tana ta zama "muhimmin wurin" yin binciken Nanometre na kasar Sin. (Umaru)


1  2  3