Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2005-12-08 17:20:04    
Kimiyyar nanometre ta kasar Sin

cri

Bayan da aka shafe shekara daya da 'yan watanni ana ta yin gine-gine, an riga an kafa wata cibiyar yin binciken kimiyyar Nanometre ta kasar Sin bisa mataki na farko wadda take da cikakken tsari da nuna manufar bude kofa da hadin gwiwa, kuma ta sha bamban da na sauran hukumomi masu yin bincike na kasar, sabo da haka wani halin samun bunkasuwa tare wajen binciken kimiyyar namometre ya bullo a duk kasar Sin.

Wannan cibiyar yin binciken kimiyyar nanometre kuma ta sha bamban da sauran cibiyoyi wadanda shugabanninsu ne ke kula da harkokin, amma wannan cibiya ta kafa tsarin daukar nauyi bisa wuyan direkta. An sami direktan cibiyar ta hanyar ba da sanarwa a fili, wanda tsawon lokacin aikinsa shekaru 4 ne. Domin kara yin hadin gwiwa a tsakaninta da kasashen duniya, cibiyar kuma ta samu "direktan kasashen ketare" ta hanyar sanarwa, kuma ta kafa kungiyar 'yan kimiyya ta farko.

Domin fara ayyukan bincike tun da wuri, cibiyar binciken kimiyyar Nanometre ta kasar Sin ta yi hayar dakunan yin binciken kimiyya na wucin gadi, kuma an gina dakunan yin gwaje-gwaje a farkon lokaci, an riga an samu sakamako bisa mataki na farko wajen gina dakunan binciken ilmin abubuwa masu rai da likitanci.

1  2  3