Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2005-12-08 17:20:04    
Kimiyyar nanometre ta kasar Sin

cri

Kimiyyar nanometre tana daya daga cikin fannonin da ake yin matukar kokari don yin bincike a kan su yanzu a duniya, kuma kasar Sin tana daya daga cikin kalilan din kasashen duniya wadanda suka fara yin binciken wannan kimiyya tun farkon lokaci, amma har ila yau tana da matsalar kasa karfin yin bincike wajen kayayyaki da mutane.

Domin kyautata kungiyoyin binciken kimiyyar nanometre na kasar Sin, a ran 31 ga watan Disamba na shekarar 2003, an kafa cibiyar binciken nanometre ta cibiyar binciken kimiyya ta kasar Sin, ban da wannan kuma jami'ar Beijing da ta Qinghua sun ba da shawara cikin hadin gwiwa don kafa cibiyar binciken kimiyyar Nanometre ta kasar Sin, gwamnatin kasar kuma ta ware kudin Renminbi Yuan miliyan 180 domin yin muhimman gine-gine da sayen na'urori da kayayyaki.

Kang Kejun, mataimakin direktan cibiyar, kuma mataimakin shugaban jami'ar Qinghua ya ce, "Tun farko an tabbatar da cewa, ya kamata a kafa wani dandalin jama'a ga duk kasar Sin har ma ga duk duniya baki daya domin sa kaimi ga yin binciken kimiyya daga fannoni daban-daban, ta yadda za a more kayayyaki da sadarwa."

1  2  3