Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2005-12-07 17:39:47    
Wasu labaru game da wasannin motsa jiki(1/12-7/12)

cri

An kawo karshen karon karshe na gasar cin kofin Davis ta wasan kwallon tennis ta shekarar 2005 a birnin Bradislafa na kasar Slovak a ran 4 ga wannan wata. Kungiyar wasan kwallon tennis ta kasar Croatia ta lashe kungiyar kasar Slovak da ci 3 da 2, ta zama zakara, wannan ne karo na farko da kungiyar Croatia ta ci kofin Davis.

An rufe gasar fid da gwani ta kwallo mai laushi ta mata ta yankin Pan-America ta karo ta 6 a birnin Guatemala, hedkwatar kasar Guatemala a ran 3 ga wata. Kungiyar kasar Amurka ta lashe kungiyar kasar Canada 2 ba ko daya, ta sake zaman zakara a jere a cikin wannan gasa, ta haka kungiyoyin kasashen Amurka da Canada da Cuba da Columbia da kuma Venezuela za su shiga gasar fid da gwani ta kwallo mai laushi ta mata ta duniya da za a yi a nan birnin Beijing a shekarar 2006.(Tasallah)


1  2  3