Za a yi gasar cin kofin duniya ta wasan kwallon badminton ta shekarar 2005 a birnin Yiyang da ke tsakiyar kasar Sin daga ran 15 zuwa ran 18 ga watan Disamba. Wani jami'in kwamitin shirya wannan gasa na Yiyang ya bayyana a kwanan baya cewa, an riga an yi kusan kawo karshen aikin share fage. a gun wannan gasar da za a yi, a karo na farko ne 'yan wasa za su kara da juna don neman samu maki 21. Gasar cin kofin duniya tana daya daga cikin manyan gasanni na koli da Hadaddiyar Kungiyar Wasan Kwallon Badminton ta Duniya ta yi.
An kammala gasar cin kofin zakara ta wasan hoki a fili ta mata ta duniya a birnin Canberra na kasar Australia a ran 4 ga watan Disamba, kungiyar kasar Sin ta lashe kungiyar kasar Argentina da ci 11 da 10, ta zama na uku. Kungiyar kasar Holland ta lashe kungiyar kasar Australia da ci 5 da 4, ta zama zakara. Yanzu a kan yi gasar cin kofin zakara ta wasan hoki a fili ta mata ta duniya sau daya a ko wace shekara, kungiyoyi mafi nagarta su kan yi karawa da juna.
1 2 3
|