Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2005-12-07 17:39:47    
Wasu labaru game da wasannin motsa jiki(1/12-7/12)

cri

A gun taron bayar da labaru kan wasannin Olympic na Beijing da aka yi a ran 5 ga wata, kwamitin shirya wasannin Olympic na Beijing ya fayyace cewa, zai fara aiwatar da shirin masu sayar da kayayyaki ga wasannin Olympic na Beijing a tsakiyar kwanaki 10 na watan Disamba, tun daga ran 12 ga wata kwamitin zai fara tattara masu sayar da kayayyaki. Shirin tallafawa wasannin Olympic na Beijing na shekarar 2008 yana kunshe da abokan yin hadin gwiwa da uban tafiya da kuma masu bayar da kayayyaki.

An yi bikin jefa kuri'a na kungiya kungiya na gasar fid da gwani ta wasan kwallon raga wato volleyball ta duniya ta shekarar 2006 a birnin Tokyo na kasar Japan a ran 29 ga watan Nuwamba, an mayar da kungiyar mata ta kasar Sin kamar gogaggun 'yan wasa a cikin kungiyar B, sa'an nan kuma akwai kungiyoyin kaasashen Rasha da Jamus da Dominica da Mexico da kuma Azerbaijan. Kungiyar maza ta kasar Sin kuma tana cikin kungiyar A, tare da kungiyoyin kasashen Japan da Masar da Poland da Argentina da kuma Porto Rico. Za a yi wannan gasa a kasar Japan a karshen watan Oktoba mai zuwa, inda kungiyoyin maza guda 24 za su yi takara da juna, yayin da kungiyoyin mata guda 24.

1  2  3