Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2005-12-06 17:30:34    
An yi yawon shakatawa a tsohon gari Nanxun na kasar Sin

cri

Idan ka zo garin Nanxun, ko shakka babu, Kauyen Liaolianzhuang zai jawo hankalinka sosai, amma ban da wannan wuri kuma, kamata ya yi ka ziyarci wata hasumiya da ke da dakuna 100. wata jagora Malama Zhang Qian ta gaya mana cewa, shekarun hasumiyar sun zarce dari 400 da aka gina, da farko dai, 'yan matan gida 100 da suka bauta wa wani babban mutum na Nanxun a zamanin da sun yi zama a hasumiyar. Ta ce,'Kafin shekaru sama da 400, wani jami'in garin Nanxun Dong yana son auren yarinyar Mao. Amma Mao ta ce, gidajen Dong ba su yi fadi sosai ba, har 'yan matan gida 100 da suka bautawa yarinyar ba su da wurin kwana. Amma Dong ya ce, ba kome, ya iya gina dakuna 100 nan da nan, ko wace yarinyar gida ta iya zaben daya. Wannan ita ce hasumiyar da ke da dakuna 100 a yanzu.'

Ko da yake a halin yanzu dai, 'yan matan gida ba su zama a hasumiyar ba, kuma ba ta da dakuna 100 ba kamar da, amma tana da alamunta na musamman na kauyen ruwa da ke kudancin kasar Sin.(Danladi).


1  2  3