A cikin lardin Zhejiang da ke gabashin kasar Sin, ya kasance da wani sararin kasa mai suna Jiahu, a wurin ana fi samar da kifaye da shinkafa kuma da siliki masu yawan gaske. Nanxun wani tsohon gari ne da ke sararin kasa, mutanen wurin sun yi arziki sosai a da, har yanzu dai ana kiyaye lambuna fiye da 20 da 'yan kasuwa masu kudi na wurin suka kafa a zamaninsu.
Shekarun garin Nanxun ya zarce dari bakwai da aka gina, haka kuma yana da dogon al'adu da kyawawan wurare masu ban sha'awa. Hanyoyin kogi suna ratsa garin, sabo da haka ne ana gina tituna da gidanje a bakin kogin. Titunan ba su yi fadi ba, kofofin kantunan a kan titunan kanana ne da aka yi da katako, ana rataya fitilu a karkashin matarin ruwa na kofofin, duk wadannan abubuwa suna kago wani tsohon yanayi mai zaman lafiya. Wani 'dan wurin Malam Zhang Xifu ya bayyana cewa, a wannan garin da fadinsa bai kai muraba'in kilimita 3 ba, ya kasance da 'yan kasuwa masu yawan gaske a da. Ya ce,'Ko da yake fadin wurinmu bai yi yawa ba, amma ya kasance da 'yan kasuwa masu kudi da yawa, mutane 12 da ke cikinsu suna da azurfa da yawansu ya zarce kilogiram dubu 50.'
1 2 3
|