Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2005-12-06 17:30:34    
An yi yawon shakatawa a tsohon gari Nanxun na kasar Sin

cri

Tun daga karni na 17, 'yan kasuwa na garin Nanxun sun fara yin cinikin siliki, sabo da haka ne Nanxun ya yi suna sosai a kasar Sin. Kafin shekaru 180, an riga an sayar da siliki zuwa kasashen India da Massar da Sham da dai sauransu. Wannan cinikin siliki ya samar wa 'yan kasuwa kudi mai yawan gaske, sai sun gina wasu manyan gidaje a garin domin nuna dukiyarsu.

Kauyen Liaolianzhuang shi ne gidaje na iyalan Liu Yong, wanda yake fi da kudi a zamanin da a wurin, kauyen shi ne lambu da ya fi girma da ake kiyaye har zuwa yanzu. Iyalan Liu sun gina wadannan gidaje masu fadin muraba'in kilimita dubu 17 ne cikin shekaru fiye da 40. A arewacin Kauyen Liaolianzhuang, akwai wani rafi mai suna Zhegu, a bakinsa an dasa wani babban itace, a kan rafin Zhegu, sai wata gada mai siffar bakar gizo da aka yi da dutse. A cikin Kauyen Xiaolianzhuang, muna iya ganin kyawawan itatuwa da furanni da gine-gine iri daban daban. Wata 'yar yawon shakatawa Malama Li Bei ta gaya mana cewa, tana son tsarin kauyen sosai. Ta ce,'Kauyen Xiaolianzhuang yana da ruwa da duwatsu, yana da itatuwa da furanni, har ma yana da gine-gine iri daban daban, dukkansu abu ne na musamman da lambunan da ke kudancin kasar Sin suke da su. Wannan shi ne abin da nake so ke nan.'

1  2  3