Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2005-11-18 17:31:08    
Wani muhimmin taron duniya kan ba da taimako ga Pakistan kan ayyukan sake gina kasar bayan girgizar kasa

cri

A cikin wannan babbar girgizar kasa da ta faru a kasashen Afirya ta kudu, yawan 'yan kasar Pakistan da suka rasa rayukansu ya zarce dubu 73. musamman ma halin da jihohin da ke arewa maso yammacin kasar da kuma shiyyar Kashmir suke ciki ya fi tsanani. Bisa kididdigar da aka bayar, an ce, kauyuka fiye da dubu 120 na shiyyoyin nan biyu sun gamu da bala'in, wanda ya taka mumunar rawa ga zaman mutane kusan miliyan 6. Kuma sabo da lokacin dari yana zuwa, shi ya sa ayyukan taimakon agaji suna fuskantar hali mafi tsanani. Bugu da kari kuma, cikin gaggawa ne ana bukatar warware batun abinci da magani da ruwan sha da kiwon lafiya da dai sauransu.

Sabo da haka, kungiyoyin duniya da kungiyoyin da ba na gwamnati ba masu yawa, ciki har da Majalisar Dinkin Duniya, da kuma kasashe da yawa da ke hada da kasar Sin nan da nan ne sun jigila kayayyakin agaji da kuma aika da kungiyoyin taimakon jiyya zuwa yankunan da ke fama da bala'i. Ban da wannan kuma, sabo da taimakon da asusun yara na Majalisar Dinkin Duniya ya bayar, an sake kafa makaranta 33 a cikin yankunan da ke fama da girgizar kasa na jihohin arewa maso yammacin kasar, da kuma makarata 10 na shiyyar Kashmir. Amma wani jami'in asusun yara na Majalisar Dinkin Duniya ya bayyana cewa, ya zuwa yanzu yara dubu 960 suna fuskatar barazanar rashin damar ci gaba da karatu.


1  2  3