An tsai da yin taron kasashen duniya kan ba da taimako ga kasar Pakistan wajen ayyukan sake gina kasar bayan girgizar kasa a ran 19 ga wata a birnin Islamabad, babban birnin kasar Pakistan. Bisa sanarwar da bangaren Pakistan ya bayar, an ce, babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya Kofi Annan da manyan kungiyoyin wakilai na kasashe da kungiyoyin duniya fiye da 60 za su halarci taron.
A ran 17 ga wata, bayan da Kofi Annan ya isa birnin Islamabad, ya yi jawabi, inda ya yi kira ga kasashen duniya da su kara ba da taimako ga kasar Pakistan bayan da girgizar kasa da ta faru a kasar. Kafin wancan rana, shugaban kasar Pakistan Musharaff ya bayar da sanarwar cewa, bankin duniya da bankin raya Asiya da kuma gwamnatin kasar Pakistan sun yi kimantawa ga babbar girgizar kasa da ta faru a Pakistan a ran 8 ga watan Oktoba, cewa kasar Pakistan tana bukatar dalla biliyan 5.2 kan ayyukan taimakon agaji da zaunar da masu fama da bala'i da kuma sake gina kasar bayan girgizar kasa. A ciki, za a yi amfani da dalla biliyan 3.5 wajen sake gina kasar, dalla biliyan 1.5 wajen ba da taimakon agaji, kuma dalla miliyan 100 wajen zaunar da masu fama da bala'i. Amma bisa kididdigar da gwmanatin kasar Pakistan ke bayar, an ce, ya zuwa yanzu yawan kudin agaji da kasashen duniya suka yi alkawarin bayar ga Pakistan ya kai kusan dalla biliyan 2.5 kawai, wanda bai iya biyan bukatun ayyukan agaji ba. Sabo da haka, Mr. Musharaff yana fatan kasashen duniya za su iya bayar da taimakon kudi ga Pakistan a gun taron duniya na ba da taimako ga Pakistan kan ayyukan sake gina kasar bayan girgizar kasa domin ta fito da mawuyacin halin da suke ciki.
1 2 3
|