Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2005-11-15 15:41:20    
Dajin duwatsu mai suna Wansheng, dajin duwatsu ne mafi dadewa a kasar Sin

cri

Tun can zamanin da, kakanni-kakannin 'yan kabilar Maio sun fara sanya tufafi masu launuka iri-iri, ya zuwa yanzu dai ma 'yan kabilar suna da irin wannan ala'dar gargajiya. Maza 'yan kabilar su kan sanya babbar riga mai launin baki wadda aka yi mata ado a bakinta, mata kuma su kan daura rawani mai launi da aka yi musu ado da lu'ulu'u a ka. Sa'an nan su kan daura rob tare da dan kwali da aka yi musu surfani a kugunsu. Da ka gan su, sai ka ce, kai, 'yan kabilar Maio suna sanye da tufafi masu kyan gani kwarai.

Ban da tufafinsu masu kayatarwa, 'yan kabilar Maio sun kware wajen yin wake-wake da raye-raye. Suna rera wakokin da sauri, amma da dadin ji ainun, haka kuma 'yan wasannin fasaha su kan rera wake-wake tare da raye-raye. Masu yawon shakatawa da yawa su kan yi sha'awar wadannan abubuwansu kwarai daga gaske. Bayan da Malam Zhou Jian ya ji wake-wake da 'yan kabilar Maio suka rera, kuma ya more idonsa da raye-raye da suka yi, sai ya yi farin ciki da bayyana cewa, ba ma kawai dajin duwatu na da ban mamaki ba, hatta ma ina sha'awar dabi'un gargajiya na karamar kabilar Maio ainun. Yayin da kake zama a wannan wuri, sai ka ji kamar kana zama a cikin aljanu ne, ka sha daularka sosai. (Halilu)


1  2  3